//
Wednesday, April 1

State TV ta Iran tace harin kasar ya hallaka “Yan ta’addar Amurka” 80

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Gidan Talabijin na State TV dake kasar Iran , ya bayyana cewa harbin makami mai linzami da kasar tayi ya hallaka dakarun Amurka da ”yan ta’addar Amurka’ dake kasar Iraqi.

State TV tace majiyarta ta cikin dakarun juyin juya hali na kasar Iran sun bayyana mata cewa, kasar tana cike da shirin sake harba wasu makamai masu linzami guda 100 idan Amurka tace zata rama harin da kasar ta kai.

Haka zalika Reuters ta sashin kasar IRAN ta rawaito daga State TV cewar harin ya lalata wasu jirage masu saukar ungulu da wasu makaman dakarun sojin Amurka.

A farkon daren ranar larabar 8 ga Janairu ne dai kasar Iran ta harba makamai masu linzami zuwa sansanin dakarun Amurka dake kasar Iran a wani yunkuri na ramuwa akan kisan babban kwamandan sojin kasar, Qassem Sulaimani.

Karin Labarai

Share.

About Author

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020