Taskar Malamai

Takaitaccen tarihin Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Sheikh Dahiru Usman Bauchi, babban Malami a Najeriya, Mataimakin shugaba a kwamitin Fatawa na Najeriya, Shugaban darikar Tijjaniyya.

An haifi Sheikh Dahiru Usman Bauchi a garin Nafada da a yanzu ke cikin jihar Gombe a ranar 28 ga watan Yulin shekarar 1927.

Ya fara karatunsa a hannun mahaifinsa Alhaji Usman. Ya kuma yi karatu a hannun manyan malamai da yawa a kasar nan da wajenta.

Kafin ya cika shekaru ashirin ya haddace Al-kur’ani. Ba dadewa kuma malaman dake kusa da shi suka sakar masa fagen. Ma’ana suka gamsu ya zama gangaran (Professor of Qur’anic memorization and education).

A shekarar 1950 ya fara tafsirin al-kur’ani. Cikin 1976 aka fara sa shi a gidan rediyon jihar Bauchi. A 1980 kuma ya dawo Kaduna da yin tafsiri, kuma tin a wannan shekarar aka fara sa shi a gidan rediyon tarayya na Kaduna.

A yanzu haka yana da ‘Yaya Sama da 70 Mahaddata Qur’ani da Jikoki masu tarin yawa. Sannan yana da Makarantun Haddar Alqur’ani sama da 200 a fadin Najeriya.

Dan gane da karatun Boko wasu daga cikin yaransa akwai Daktoci da Malaman Jami’a kamar Dr, Abubakar Surumbai, Dr. Fatihi, da Marigayi Dr. Hadi wanda shine babban ‘da a wurinshi.

A halin yanzu yana daga cikin manyan malaman kasar nan. Allah kara masa lafiya da nisan kwana.

Karin Labarai

UA-131299779-2