Kwankwaso bai je jihar Ribas bayan an rushe Masallaci ba – Shiri ne da shiriritar ‘yan ‘Social Media’ – Bincike

Hotonan da ‘Yan Kwankwasiyya suke yadawa akan zuwan Kwankwaso jihar Ribas ya kwana 383 a duniya. (Shekara 1 ga kwana 20).

DABO FM ta binciko hotunan a shafin Twitter na Engr Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, wanda ya wallafa ranar 14 ga watan Agustar shekarar 2018, da misalin karfe 2:24 na rana (GMT +1, UTC +4:30) a lokacin da yake yawon neman takarar Shugabancin Najeriya.

Ana wallafa hotunan ne kan cewa, tsohon gwamnan jihar Kano, Dr Rabi’u Musa Kwankwaso ya kai ziyarar bazata zuwa jihar Ribas domin tattaunawa da gwamnan jihar, Nyseom Wike akan ruguje Masallaci da yayi a garin Fatakwal.

Kalli rubutu da hotunan a shafin Engr Kwankwaso

Masu Alaƙa  Fadan Kwankwasiyya da Gandujiyya ya fito da ‘Sabon Salo’, kashi na 2

Sako na musamman

Shin kuna da wata sanarwa ko bukatar bamu labari?

Ku aiko mana da sako ta submit@dabofm.com

%d bloggers like this: