1
Gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya bada umarnin yin ragi akan takin da manoma zasu yi amfani dashi cikin damunar bana.
Dabo FM ta rawaito gwamna Tambuwal ya bayyana hakan ya biyo bayan burun gwamnatin jihar na bunkasa aikin noma, samawa jama’ar jihar aikin yi, kamar yadda Tambuwal ya bayyana a lokacin da yake sanar da farshin da gwamnatin sa ta saka.
Da yake bada umarnin ya kuma bayyana a fitar da takin dake cikin ma’ajiyar gwamnatin jihar ta Kasarawa, dake karamar hukumar Wamakko, kana ya bayyana a baya ana saida takin N9,800.
