Tarihi: Lokacin da ake sanar da dauke Wutar Lantarki a Najeriya

Karatun minti 1

A lokacin da ake cigaba da samun matsalolin rashin wutar Lantarki a Najeriya ta awa 24, DABO FM ta binciko lokacin da ake sanar da dauke wuta a Najeriya.

A wata sanarwa da kakakin ma’aikatar a wancen lokacin, Mista Alex Nwokedi, a ranar 12 ga watan Maris na shekarar 1972 (lokacin mulkin Janar Yakubu Gowon), ya sanar da dauke wutar Lantarkin a wani sashin kudancin Najeriya.

Mista Alex ya sanar da lokacin da za’a dauke da kuma lokacin da za’a maido da wutar bisa dalilin gyara da hukumar zatayi.

“Sanarwar samun katsewar wutar Lantarki bisa gyaran kayan aiki. Za’a samu katsewar Wutar Lantarkin yankunan Akure, Yammcin Tsakiya da Enugu, a ranar Lahadi, 12 ga watan Maris, 1972 daga karfe 9:00 zuwa karfe 3:00 na Yamma.

Katse Lantarkin ta zama tilasta domin inganta kayayyakin aikinmu.”

Karin Labarai

Sabbi daga Blog