Siyasa

Yacce haduwar ‘Abba Gida-Gida’ da wakilan Ganduje ta kasance cikin aminci

Wakilan gwamnan Kano, Dr Abdullahi Ganduje da na dan takarar gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, sun hadu cikin farin da annashuwa yayin saukarsu a filin tashi da saukar jirage na Nnamdi Azikiwe dake birnin Abuja.

DABO FM ta tattara cewar a gobe Litinin, kotun kolin Najeriya zata yanke hukuncin karshe akan shari’ar zaben gwamnan jihar Kano da PDP da ‘dan takararta suke kalubalanta.

Kwamshinan kananan hukumkomin Kano, Murtala Sule Garo da Abdulmajid Dan Balki Kwamanda yayin gaisawa da Abba Kabir Yusuf. Hoton: Hon Umar Mai Wayo

Gwamnan Kano, Ganduje, shine yayi nasara a kotunan korafin zabe da ta daukaka kara.

A wasu hotuna da suke yawo a shafukan sada zamunta, an dai hangi jagororin bangaren guda biyu yayin da suke sauka a birnin Abuja, suna cike da farinciki cikin girmama juna.

Haduwar da ta sha bambam da irin wacce ke hada masoyan wadannan jagorori duk da cewar sun fi kusa da kawunansu akan wandanda suke marawa baya. Haduwar magoya bayan da kusan mafiya yawan loktu take haddasa tashin hankula a tsakanin talakawan gari.

Hakan ne ma yasa aka dade ana kira ga al’umma da su kaunaci juna, sun bar illata junansu akan soyayya ko goyon bayan wani dan siyasa da kansu da su da ‘ya’yansu suke zama lafiya.

Karin Labarai

Masu Alaka

‘Yan sanda sunyi alkawarin kama duk masu hannu a yiwa Pantami ihun ‘Bamayi’

Muhammad Isma’il Makama

Kotun daukaka kara ta baiwa ‘Abba Gida-Gida’ damar kara shedu a cigaba da shari’arshi da Ganduje

Dabo Online

‘Yan Kwankwasiyya sun dauki hanyar kawo wa Shari’ar ‘Abba Gida-Gida’ cikas

Dabo Online

Yanzu-Yanzu: Jiga-jigen APC sun dira a Habuja da duku-duku kan shari’ar zaben Kano

Muhammad Isma’il Makama

Kotun Koli: Farfaganda baza ta canza abinda Allah ya tsara ba -Abba ya yiwa Ganduje martani

Muhammad Isma’il Makama

Sakamakon zaben Gama ya ɓace ne a cibiyar tattara sakamako dake karamar hukuma – Baturen Zabe

Dabo Online
UA-131299779-2