Tarihi: Sarkin Musulmai Sir Abukabar III ne ya rada wa kungiyar IZALA suna

dakikun karantawa

Kungiyar Jama’atu Izalatul Bidi’a Wa Ikamatu Sunnah, kungiyace ta addini Musulunci a Najeriya wacce wanda ya kafa ta, Marigayi Sheikh Isma’ila Idris, dan jihar Kano ya kafa a shekarar 1978.

Duk da cewar ana Sheikh Abubakar Gumi ya fi suna akan harkokin kungiyar IZALA, DABO FM ta bincika cewar Marigayi Sheikh Isma’ila ne ya kirkiri kungiyar.

Sir Abubakar Siddiq na 3, Sarkin Musulmai na 14 a tarihin shugabancin musulmin Najeriya da wasu kasashen yammacin Afirika ne ya bada gudunmawar sunan kuniyar Izala a Najeriya, kamar yadda Marigayi Sheikh Auwal Albani Zari ya fada a wani karatun na tarihin kungiyar Izala.

Sheikh Albani ya bayyana cewar, Mallam Isma’ila yaje wajen Sarkin Musulmi, Sultan Abubakar III domin neman tabarruki da addu’a akan kafa sabuwar kungiyar da aka tilasta masa kafawa kafin ya cigaba da karantarwa.

“Ya je wa sarkin musulmi cewar zai kafa kungiya mai taken Izalatul Bidi’a” – Marigayi Sheikh Auwal Albani.

Ya kara da cewa, Sarkin Musulmi, Sir Abubakar II yace wa Sheikh Isma’ila, kayi kuskure idan ka gusar da bidi’a kuma baka tsaida sunna ba, meyasa bazaka kara ‘Wa Ikamatus Sunnah ba’?”

“Daga nan sai ya karba, daga nan yaje yana kiran kungiyar da Jama’atu Izalatul Bidi’a Wa Ikamatu Sunnah.”

A wani bincike da Dr Ramzi Ben Amara, malami a sashin musulunci na jami’ar Cape Town dake kasar Afirika ta Kudu, ya bayyana kafuwar kungiyar Izala bisa jajurcewa da kokarin da Sheikh Isma’ila yayi wanda ya jawo cece kuce a wancen lokacin.

Binciken Dr Ramzi mai taken Shaykh Ismaila Idris (1937-2000), the Founder of the Izala movement in Nigeria, In: Annual Review on Islam in Africa, Vol.11, pp. 74-78, 2012, ya bayyana wasu sauye-sauye da dan karamin rudani da kafuwar kungiyar ya kawo wanda ya kira da “Rabuwar Najeriya da Sufanci, wanda har ta kai ga malamin yayi fatawar ‘A dena cin yankan da masu bin Sufanci suka yi.

Haka zalika, ya bayyana Sheikh Isma’ila a matsayin wanda yayi kokarin cigaba kira zuwa ga addinin Musulunci a sassan Najeriya har lokacin da yana jami’an Sojin Najeriya.

Sheikh Isma’ila ya shiga aikin Soja biyo bayan labarin mayar da wani Masallaci zuwa wajen shan giya a cikin barikin Sojoji dake garin Kaduna. A aikinshi na Soja, ya kasance limami da mai yada da’awa a tsakani abokan aikinshi na Soja da sauran mutanan gari.

Bafulatani dan asalin jihar Kano kuma mazaunin jihar Bauchi, ya rasu a shekarar 2000. Ya rasu ya bar mata hudu da ‘ya’ya 10.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog