//
Wednesday, April 1

2023: Akwai yiwuwar rugujewar APC bayan mulkin Buhari -Fayemi

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Gwamnan jihar Ekiti karkashin tutar jam’iyyar APC, Kayode Fayemi ya bayyana akwai yiwuwar rugujewar jam’iyyar sa ta APC bayan zangon mulkin shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Mijiyar Dabo FM ta bayyana Fayemin yayi wannan batu ne a lokacin da wani rahoto ya fito na kokarin wasu gwamnoni na sai sunga an tsige shugaban jam’iyyar APC ta kasa, Adams Oshiomhole.

A Nuwanbar da ta gabata ne dai tsagin APC dake goyon bayan gwamnan Edo, Godwin Obaseki ta dakatar da Oshiomholen bayan an gudanar da kada kuri’ar rashin goyon baya.

Fayemi ya kara da cewa “Idan bamuyi taka tsan-tsan ba kuma bamuyi tsarukan da zasu kaimu gaci ba, jam’iyyar mu zata ruguje bayan zangon mulkin Buhari, saboda shine jigon jam’iyyar.” Kamar yadda DailyTrust ta bayyana.

Karin Labarai

Share.

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020