Tsohon shugaban Majalisar Matasan Nijeriya yayi kira ga Matasa su guji siyasar ‘A mutu ko ayi Rai’

Minna, jihar Niger.

Tsohon Shugaban Majalisar Matasan Nijeriya, kuma mai sharhi a kan lamuran yau da kullum Kwamared Abdullahi Abdulmajeed, ya shawarci Matasa su guji siyasar a mutu ko a yi rai ko kuma siyar da kuri’ar su musamman a ranar zabe.

Kwamared Abdullahi, ya kwatanta yin hakan a matsayin wani babi na rashin sanin mutumci da darajar Kai, kuma hakan sam ba zai kai Kasar nan da matasan ta ga tudun mun tsira ba.

Abdullahi Abdulmajeed ya bayyana haka ne a jihar Nijar, sa’ilin da yake gabatar da kasida a taron da magoya bayan Lolo suka shirya a dakin taro na Idris Kutigi da ke Minna, domin duba matsalolin matasa da lalubo hanyar magance su.

Masu Alaƙa  Borno ta doke Kano a zabe na 2 a gasar Kwalliyar Al’adu bayan ayyana zaben farko ‘Inconclusive’

Ya ce, kasa kamar Nijeriya, a yau da mafi akasarin al’ummar cikin ta Matasa ne, amma akwai takaici kwarai da gaske a samu matasan na aikata wasu abubuwa da sam baya cikin tsari da kyautata tarbiyar su.

Ya kara jaddada goyon bayan sa ga Matasa da su shiga harkar siyasa a dama da su, domin su ne kashin bayan ci gaban kowacce al’umma.

Abdullahi Abdulmajeed, ya kara da cewa, a halin da kasar nan ke ciki fa dole ne matasa su tashi tsaye kuma a dama da su ta hanyar kawo sauyi mai ma’ana da kuma tafiya da zamani.

“A matsayin matashi dole kullum ya rika sanya tunanin hanyoyin da zai bi wurin kawo kyakkyawan ci gaba a kasar shi, saboda sauran masu tasowa” inji Kwamared Abdullahi.

Masu Alaƙa  Hoton 'soyayya' na Baturiyar Amurka da dan Kano a dakin Otal ya janyo cece kuce

Inda ya yaba wa Gwamnan Jihar Nijar Abubakar Sani Bello, saboda irin gudunmuwa da ya bayar wurin ci gaban Matasa a Jihar sa, A matsayin sa na matashi, sannan ya yi fatan sauran gwamnoni su dauki salon jagorancin sa domin ci gaban kasar nan baki daya.

Karin Labarai

Leave a Reply

Your email address will not be published.