Da dumi-dumi: An ga diyar dan Majalissar Kano da aka yi garkuwa da ita

Karatun minti 1

An samu nasarar samun ‘yar gidan, Hon Murtala Musa Kore, dan majalissa mai wakilar karamar hukumar Dambatta a majalissar jihar Kano, a daren ranar Talata, DABO FM ta tabbatar.

A ranar Lahadi da misalin karfe 3 na dare, wasu ‘yan bindiga suka kutsa gidan dan majalissar a garin Kore dake karamar hukumar Dambatta a jihar Kano , suka yi awon gaba da ‘yar tashi mai suna Juwairiyya Murtala Musa Kore da ake kira ‘Mommy’

Iyalan dan majalissar da babban mataimakin dan majalissar a fannin yada labarai, Hon Murtala Najmur ne suka tabbatar wa DABO FM.

“Allah Ya bayyana Mommy a jiya Talata da misalin karfe 2 na dare, an same ta a hanyar Mai Gatari ta jihar Jigawa. Mutanen da ba a san ko suwaye ba ne suka shiga gidan wanarabul suka yi awon gaba da ita. To Allah ya dawo mana da ita yanzu.” – in ji Hon Murtala Najmur.

Ya yin zantawar dan majalissar da sashin Hausa na BBC, ya shaida cewa ‘yan bindigar sun je gidansa ne domin su sace shi, lamarin da suka iske shi ba ya nan.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog