Labarai

Wallahi zan auri Babangida ko ‘Kwarkwara’ zai yi dani – Budurwa mai son IBB

Biyo bayan bayyana neman aure da tsohon shugaban Najeriya, Janar Babangida yace yanayi, mata dayawa sun nuna sha’awar auren IBB.

A wata tattaunawa da Janar Babangida yayi da jaridar Sun wacce aka wallafa a jiya Asabar, IBB ya sha’awarshi kan samun matar aure “kafin lokacin tsufa yazo” masa – Kamar yacce ya bayyana.

DABO FM ta tattaro tururuwar yan mata musamman na Arewa da suka nuna sha’awarsu akan auren tsohon shugaban kasa a kafafen sada zumunta.

Daga cikin mata akwai wadanda suka aike mana da sakonni a kan shafin mu na Facebook da wadanda suka bayyana sha’awar tasu a dandalinmu na muhawarar Facebook.

Kadan daga cikin sakonnin da muka samu akan ‘Facebook‘ da ‘Whatsapp

Wacce ta bukaci mu boye sunanta ta shaida cewa; “Ya samu, yazo zan aure shi. Ko an riga ni, Allah ya halartawa namiji auren Mata 4, to babu damuwa zan iya zama ta hudu. Wallahi ko a kwarkwara ba damuwa, ballantana ma yana kallo na zai “hola”.

Wata mai suna Maryam tace; “Ni babba ce yazo zan auresa”

Daga dandalinmu na Facebook kuwa, mun samu sakonni kamar haka;

Imanatu tace; “Gani abi ni lambarshi ko ayi mishi magana.

Hadiza; “Gani, kuma shekaruna sun ja, inaga watakila ko yar shekara 59 tayi maka, amma ni ‘yar talakawa ce.”

Zahra; “Hh, aurenso nake so ba na kudi ba.”

Binta; “Ka nema da kanka.”

Sai dai a nashi bangaren, Janar Babangida ya bayyana cewa zan yi adalci wajen kin auren budurwa domin kada ya takura wa rayuwarta.

Karin Labarai

Masu Alaka

Ina nan da raina ban mutu ba – IBB

Dabo Online
UA-131299779-2