//

Rikicin Masarautu: Masu nada Sarki sun kara maka Ganduje a kotu

0

Babbar kotun tarayya dake jihar Kano ta sanya ranar 17 ga watan nan domin fara sauraron karar da masu nada Sarki suka shigar.

Karar dai na kalubantar kafa sabuwar dokar kafa Masarautu ta 2019 bayan rushe tsohuwar da kotu tayi, an shigar da karar ne ranar 4 ga Disamba.

Dabo FM taci karo da wata takarda data bulla mai lamba SUIT No.K/197/2019, wadda kotu ke sanar da ranar da zata fara sauraron wannan kara da masu nada Sarkin suka shigar.

Suna zargin cewa a wannan karon ma ba’a bi doka wajen Samar da masarautun ba, domin kuwa an samar dasu ne duk da umarnin wata kotu da ya hana yin hakan.

Masu Alaƙa  Abubuwan da zasu iya faru wa in Sarki Sunusi ya ketare wa’adin Ganduje

Masu shigar da karar sun hada da

 1. Sarkin Ban Kano, Mukhtar Adnan.
 2. Madakin Kano, Yusuf Nabahani.
 3. Makaman Kano, Abdullahi Sarki Ibrahim.
 4. Sarkin Dawaki Mai Tuta, Bello Abubakar.

Wadanda ake kara sune:

 1. Gwamnan Kano
 2. Kakakin Majalisar Kano
 3. Majalisar Kano
 4. Atoni Janar
 5. Aminu Ado
 6. Ibrahim Gaya
 7. Tafida Abubakar Ila
 8. Dr. Ibrahim Abubakar II

Karin Labarai

Share.

Comments are closed.

%d bloggers like this:
©Dabo FM 2020