An yi kira ga al’ummar yankin karamar hukumar Zariya da ke Jihar Kaduna, su cigaba da bin dokokin kasa sau da kafa, tare da sanar da Jami’an Tsaro duk wasu abubuwan da ke faruwa a tsakanin su cikin sauri domin daukar matakan da suka dace saboda tabbatar da doka.
Wani jigo a Jama’iyyar Apc a gundumar Gyallesu Injiniya Ado Bebeji shi ne ya bayyana hakan sa’ilin zantawar sa da Dabo FM a Zariya.
Jigon na Jama’iyyar Apc wanda har ila yau shi ne mataimakin sakataren Jama’iyyar a gundumar ta Gyallesu, ya ce bukatan hakan ya zama dole duba da yadda gwamnati ke iya bakin kokarin ta a koda yaushe domin kare lafiya da dukiyoyin al’ummar ta.
Ya ce, sanar da Jami’an tsaro cikin gaggawa zai taimaka wurin kawo dauki duk lokacin da wani abu ke faruwa.
Sai dai ya naimi ganin gwamantin ta cigaba da wadata Jami’an tsaron da kayayyakin da suka dace domin fuskantar kowanni kalubale.
Da ya juya ta bangaren Jami’an tsaron kuwa, ya tunatar da su muhinmanancin da ke akwai gare su, su cigaba da aiki tukuru domin cika alkawarin da suka yi na kare lafiya da dukiyar kowanne dan kasa.
Injiniya Ado Bebeji, ya yabawa Gwamnatin Tarayya, da ta Jihar Kaduna, da Majalisar masarautar Zazzau, saboda kokarin da suke koda yaushe na kula da tsaron al’umma.
A bangare guda kuma, Hon Injiniya Ado Bebeji, ya yi tsokaci akan cutar COVID-19 da ta addabi duniya a yau, Kuma ya bukaci al’umma su kasance masu bin umarni da shawar-warin gwamnati da na masana kiwon lafiya musamman game da cutar COVID-19 da ya addabi al’umma a fadin duniya.
Ya ce, duk lokacin da aka samu wata musiba a gari babu mafita illa a koma a dangana lamarin ga Allah madaukakin Sarki, tunda shi ne kawai mai yaye dukkanin musibu da fitinu da suke damun al’umma.
Ya nuna bakin cikin sa ganin wadda suka kamu da wannan cuta harda mai girma gwamnan Jihar Kaduna Nasiru Ahmed El-rufa’i, kuma ya yi masa fatan samun koshin lafiya da ma sauran wanda suka kamu da cutar domin cigaba da gudanar da al’amura kamar yadda aka saba.
Ya kara da cewa,tun bayan bullar cutar ta COVID-19,masana kiwon lafiya sun yi ta shawartan al’umma su dauki matakin kare kan su daga balahiran wannan cuta, da suka hada da wanke hannu akai-akai da kaucewa shiga taruwan jama’a da kuma daukan duk wasu matakai da zai zama rigakafin kamuwa da cutar.
