Harin Nubapoly-Asup ta koka

dakikun karantawa

Tun bayan harin da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne suka kai a makarantar Nuhu Bamalli da ke Zariya ta Jihar Kaduna wanda ya yi sanadiyyar sace mutane Biyu tare da jikkata wani ma’aikacin makarantar Daya, Kungiyar malamai ta makarantar wato Academic staff union of polytechnic ASUP, ta koka kan halin da makarantar ke ciki tsawon shekaru da suka gabata.

Shugaban kungiyar Injiniya Aliyu Musa Kofa, ya yi koken lokacin da ya kira taron manema labarai a sakatariyar kungiyar kan abun da ya faru a karshen makon.

Ya ce, makarantar ta jima tana fama da matsaloli bangaren koyo da koyarwa na rashin isassun kayayyaki da kuma killace makarantar ta bangaren kudu da yammacin ta, wanda yana daya daga cikin dalilan da ya baiwa batagarin daman shigowa makarantar ba tare da fargaba ba har suka yi awon gaba da mutane uku, ciki kuwa har da memba a kungiyar mai suna Injiniya Bello Atiku da yara biyu.

Ya Kara da cewa, duk da gwamanti ta samar da wasu gine-gine da hanyoyi a cikin makarantar, akwai bukatar ta sake duba halin da ake ciki domin samar da tsari mai kyau ga ma’aikata da daliban da suke karatu a makarantar.

A cewar Injiniya Aliyu Kofa, duk da akwai rashin kudi da ake fama da shi a Jihar Kaduna, wannan ya haifar da rashin samar da isassun kayayyakin da ake bukata cikin lokaci.

“In zaku iya tunawa a shekarar da ya wuce, batagarin sun taba shigowa sun yi awon gaba da wata ma’aikaciyar wannan makaranta, Kuma ta dalilin haka ne aka samar da yan sandar kwantar da tarzoma a makarantar domin kula da harkar tsaro. Duk da suna iya bakin kokarin su, sai dai basu da yawan da za su iya bada kariyar da ake bukata a ciki da wajen makarantar”, a cewar Shugaban.

Kuma suna iya bakin kokarin su matsayin su na kungiya suna tattaunawa da bangaren jagororin makarantar da gwamanti da duk masu ruwa da tsaki domin ganin an saki wanda aka kama sun koma cikin iyalan su lami lafiya.
Tunda tun washe garin ranar da abun ya faru, kwamishinan Ilimi na Jihar Kaduna da Dan majalisa mai wakiltan cikin Birnin Zariya da shugaban ‘yan sanda shiyya ta Daya da ma sauran masu ruwa da tsaki a harkar tsaro duk sun zo makarantar kuma sun ga halin da ake ciki, suka kuma yi alkawarin taimakawa domin samun cigaba mai dorewa

Daga nan sai ya bukaci ma’aikata da daliban makarantar su cigaba da yin duk mai yiwuwa wurin sanya kishi da aiki tukuru domin cigaban makarantar.

Idan dai za’a iya tunawa, A daren Asabar din da ta gabata ne, wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka shiga rukunin gidajen ma’aikata na makarantar kimiyya da fasaha ta Nuhu Bamalli da ke Zariya ta Jihar Kaduna, inda suka yi awon gaba da mutane uku yayin da suke harbi daya a hannu.

Uwar gidan wanda aka yi awon gaba da shi, Injiniya Bello Atiku, wato Khadija Sulaiman ta ce mai gidan nata ya dawo gida misalin karfe tara na dare sai ya tsaya a waje ya jima yana waya da wani mai gidan sa kan wani taro da za’a gudanar. Daga bisani ya shigo cikin daki kuma suka yi kallo tare da yara har suka kwanta.
Suna zaune ne sai suka ji ana buga kofar dakin, bayan sun fito ne sai suka yi kicibis da mutane biyu dauke da bindigogi suka naimi su kwanta a tsakar dakin, Bayan sun kwanta sai suka bukaci su basu wayoyin su Kuma suka tafi da wayoyin tare da mai gidan nata wato Injiniya Bello Atiku.

Ta kara da cewa rukunin gidajen nasu yana falalar fili ne ba tare da an killace su ba, shiyasa ma suka sami daman shigowa ba tare da wani fargaba ba.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Shugaban makarantar Injiniya Dakta Kabir Abdullahi ya ce barayin sun isa kwalejin ne da misalin karfe 9 na daren Asabar kuma suka yi awon gaba da ma’aikacin nashi, Kuma suna iya bakin kokarin su domin an bankado barayin tare da dawo da shi cikin iyalan sa cikin koshin lafiya.

Shugaban ya kuma tabbatar da cewa daya daga cikin ma’aikatan, Sunusi Hassan an harbe shi a hannu wanda ya tsallake rijiya da baya daga ‘yan ta’addan suka yi yunkurin sace shi kuma an garzaya da shi asibiti don kula da lafiyarsa.

Shi ma kwamishinan Ilimi na Jihar Kaduna Shehu Usman Makarfi ya ce suna iya bakin kokarin su domin kara yawan jami’an tsaron da ke aiki a makarantar, Kuma za su cigaba da duba yiwuwan daukar matakan da suka dace domin killace makarantar.
Kuma ya naimi ma’aikata da daliban makarantar su kwantar da hankulan su yayin da za’a cigaba da gudanar da harkokin karatu kamar yadda aka saba.

Tuni dai rundunar yan sandar Jihar Kaduna ta tabbatar da faruwan lamarin ta bakin kakakin ta Muhammad Jalige.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog