News

Shugaba Buhari ya rusa Kwamatin da ya kafa na kwato kadarorin Gwamnati

President Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rushe kwamitin shugaban kasa na musamman akan dawo da kadarorin gwamnati (SPIP) wanda Mista Okoi Obono-Obla ke shugabanta.

An umurci Atoni-Janar na tarayya kuma Ministan shari’a da yayi gaggawan karban duk wani bincike da ke kasa da sauran ayyukan SPIP din.

Mukaddashin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ne ya kafa kwamitin a watan Agusta 2017, domin binciken lamuran da suka shafi rashawa, almubazaranci da sauran laifuffukan da jami’an gwamnati ke aikatawa.

Shugaban kasa Buhari ya mika godiya ga dukkanin mambobin kwanitin akan gudunmawarsu.

Shugaban kasar na duba zuwa ga karban rahoton karshe na hukumar ICPC akan binciken shugaban kwamitin da aka rushe wanda ke gudana.

Comment here