Labarai

‘Yan Bindiga sun hallaka Kyaftin da wasu Sojoji 3 a jihar Niger

Wasu yan bindiga a jihar Niger sun hallaka Sojoji 3 da Kaftin guda 1 a wata kwantan bauna da sukayi wa Sojojin a unguwar Sarkin Pawa dake karamar hukumar Munya dake jihar ta Niger.

Jaridar The Nation ta rawaito cewa sojojin da aka kashe sun hada da Kaftin, Sajan da Kofur guda 2.

Jaridar tace an kashe Sojojin ne bayan da suka fito kawo dauki bayan wani kiran waya da suka samu don kawo dauki yayin da ‘yan bindigar suka rika fakawa gidajen mutane.

Sojojin da suna fito daga sansaninsu dake Zazzaga zuwa Gwar tare da wasu jami’an ‘yan sanda a cikin mota.

Rahoton ya bayyana cewa yan bindigar sun tsere bayan ganin jami’an tsaron, suka danna cikin daji inda a nan ne sukayi kwanton baunar.

Shigarsu dajin ke da wuya aka fara jiyo harbe-harbe tsakaninsu inda a nan ne suka harbe Kyaftin din da ya jagoranci tawagar.

An shafe sama da awa 1 ana fafatawa tsakanin jami’an da ‘yan bindagar, a nan Sojoji 3 suka rasa rayukansu. – Kamar yacce jaridar ta tabbatar.

Da yake tabbatar da lamarin, shugaban karamar hukumar Munya, Alhaji Muhammad Garba Dazz, yace ‘yan bindigar da adadinsu ya kai 30 sun afko cikin kauyen tare da tsare mutanen garin kafin lokacin da Sojojin suka zo.

“Ni da kaina na sanar da Sojojin inda ‘yan bindigar suke, abin yafi karfin sojojin da ‘yan sanda saboda yawan ‘yan bindigar.

Bayan awa 1, sun fito da motarsu da harbin harsasai a jiki da gilas din a sauke.

“Sun kashe Sojoji 4, 3 daga ciki kuma sunji mummunan ciwo, sun kuma kona ‘Hilux’ din Sojojin”

UA-131299779-2