//
Wednesday, April 1

Rikicin Amurka da Iran zai zama alfanu ga Najeriya ta fannin tattalin arziki – Masana

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Tin farkon watan Janairu, rikici ya kara tsamari tsakanin kasar Amurka da kasar Iran bayan da Amurka ta kashe babban kwamandan sojin kasar Iran, Qasem Soleimani.

Masana na ganin cewa rikicin kasashen biyu zai iya haddasa hauhauwar farashin danyen man fetur a kasuwar duniya wanda ake ganin kasashe irin Najeriya za ta samu habbakar tattalin arziki.

DABO FM ta tattaro masana suna kallon rikicin Iran da Amurka a matsayin rikicin da zai shafi yankin gabas ta tsakiya da sauran kasashen duniya.

Yayin wata tattaunawa da sashin Hausa na rediyo Muryar Amurka tayi da Farfesa Bello Muhammad Bada, babban malami a jami’ar Usmanu Dan Fodio ta jihar Sokoto a arewacin Najeriya, ya bayyana yacce kasashen Afririka musamman Najeriya zasu amafana da rikicin Amurka da Iran.

Masu Alaƙa  Sojojin Amurka 34 sun sami tabin kwakwalwa bayan harin da Iran ta kai musu

Farfesa Muhammadu Bello yace ta samu kudin shiga mafi tsoka a lokacin da yakin Iraqi ya barke, inda ya kara da cewa tabbas ne farashin mai ya tashi idan rikicin Iran ya barke, kuma kashashen irinsu Najeriya zasu kara samun kudin shiga daga man da suke fitarwa.

Sai dai yace idan farashin ya tashi, itama Najeriya zata kashe kudaden dayawa wajen siyan taceccen man da ake amfani dashi a cikin kasar.

Saurari cikakkiyar hirar (Mallakar VOA Hausa)

Mallakar VOA Hausa

Karin Labarai

Share.

About Author

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020