‘Yan Bindiga sun sace ‘dan uwan Sani Mu’azu, gwamnan ‘Alfawa’ na shirin ‘Kwana Casa’in’

Masu garkuwa da mutane sun sace Salisu Mu’azu ma shiryin fim a Kannywood, dan uwan fitaccen jarumi, Sani Mu’azu na masana’antar Nollywood da Kannywood.

Masu garkuwar dai sun sace Salisu Mu’azu a jiya Juma’a a kan hanyarsu ta komawa garin Jos bayan ya halarci wani babban taro a jihar Kaduna.

Sani Mu’azu ne ya bayyana haka a shafinshi na Instagram, inda ya bayyana cewa ya samu tsallake rijiya da baya, sai dai yan bindigar sunyi awon gaba da kanin nashi da kuma wasu mutum 2 da suka dauka a motarsu zasu je jihar Bauchi.

“Jiya a hanyar mu ta komawa Jos daga Kaduna bayan wani taro, mun shiga hannun ‘yan fashi da makami ko masu garkuwa da mutane a garin Saya.”

“Sun mana fashi, na samu nasarar tserewa, sai dai kanina, Salisu Mu’azu da wasu abokai 2 da muke dauka zuwa Bauchi, Danlami Yanke-Yanke da Bature suna hannun masu garkuwar.”

“Sun tuntube mu yau da safe, suna bukatar kudin fansa Naira miliyan 10.”

“Dan Allah ku taimaka da addu’a.”

Daga shafin Adamu Zango

Daga Shafin Ali Nuhu

%d bloggers like this: