Labarai

‘Yan Kwadago sun fara gajiya da wasan buyar da gwamnati take musu akan albashin N30,000 – IPAC

Hukumar IPAC tayi kira ga gwamnati tarayya da tayi hanzari wajen tabbatar da fara biyan ma’aikata albashinsu na N30,000 domin inganta rayuwar ma’aikatan.

Shugaban hukumar na jihar Legas, Shakirudeen Olofin ne yayi kira ga gwamnatin a dai dai lokacin da yake ganawa da kamfanin dillancin labarai ta Najeriya ‘NAN’

Yace ma’aikatan Najeriya sunyi juriya matuka kan irin wahal-halun da suke sha duba da irin tsadar rayuwa da ake fama da ita.

Ya kara da cewa, yin sauri wajen tabbatar da fara biyan sabon albashin na N30,000 zai ragewa ma’aikatan radadi.

Olafin, ya yabawa shugaba Muhammadu Buhari bisa sanyawa dokar karin albashin hannu, kuma yayi kira da yayi kokari wajen tabbatar da dorewar tare da aiwatar da dokar.

“Gwamnatin tarayya tayi kyan kai sosai bayan da ta aminta bukatar kungiyar kwadago na karin albashin ma’aikata zuwa 30,000.”

“Sai dai tin watan Afirilu da aka sanyawa dokar hannu, anata samun tsaiko wajen fara biyan kudin, muna ganin cewa lallai gwamnati bata yiwa ma’aikata adalci akan wannan ba.

“Yanayi tsadar rayuwar yanzu ta linka wajen sau 6 a shekaru 6 da suka shude kuma duk da haka N18,000 ake biyan ma’aikata.

“Ma’aikata suna bukatar a duba lamarin cikin hanzari. Duk da cewa N30,000 din ma bata dace da yanayin tattalin arziki na yanzu ba.

Karin Labarai

Masu Alaka

Sai mun rage ma’aikata zamu iya biyan mafi karancin albashi – Ministan Kwadago

Muhammad Isma’il Makama

Mun gaji da gafara Sa bamu ga Kawo ba akan karin Albashin N30,000 – Kungiyar Kwadago

Dabo Online

Duk shifcin-gizo gwamnoni keyi a batun biyan Sabon Albashi -Kungiyar Kwadago

Muhammad Isma’il Makama

Sai mun rage ma’aikata zamu iya biyan mafi karancin albashi – Ministan Kwadago

Muhammad Isma’il Makama

Ma’aikatan Cross River sun nuna rashin jin dadi bisa yacce Gwamnan jihar ya albashi 1 ga wata

Dabo Online
UA-131299779-2