AFCON: Madagascar ta ragargaza Najeriya ta ci biyu da nema

A cigaba da buga gasar cin kofin nahiyar Afrika, kasar Najeriya tana barje guminta da kasar Madagascar a wasan karshe na ‘yan rukunin B.

Yanzu haka Madagascar ta zurawa Super Eagles ta Najeriya kwallaye 2 a raga.

Madagasca ta jefa kwallon fari ne a mintuna na ’13 ta hannun dan wasanta L.Nomenjanahary , kwallo ta biyu ta hannun dan wasa Andriamahitsinoro a mintuna na ’53 daga bugun tazara.

Yanzu haka kasar Madagascar ce take jan ragama a rukunin B da maki 7, yayin da Najeriya take ta biyu da maki 6, kasar Guinea tana ta 3 da maki 4 inda Burundi take ta 4 babu maki ko 1.

Kasar Madagascar da Najeriya ne zasu garzaya zagaye na 16 a cikin ‘yan rukunin Bna gasar cin kofin nahiyar Afrika.

Masu Alaƙa  'Yan Kwallon Najeriya ta mata sun samu tafiya gazaye na 16 a gasar kofin duniyaSako na musamman

Shin kuna da wata sanarwa ko bukatar bamu labari?

Ku aiko mana da sako ta submit@dabofm.com

%d bloggers like this: