‘Yan sandan jihar Jigawa sun cafke Matar da ta watsa wa Mijinta ruwan zafi a al’aurarshi

dakikun karantawaA ranar Litinin, rundunar yan sandan jihar Kano ta tabbatar da kame matar da ake zargi da kwarawa mijinta ruwan zafi bisa dalilin kara aure a garin Dambatta dake jihar Kano.

Rundunar tace tin a lokacin data samu rahotan faruwar lamarin, ta fara zaryar sumame da niyyar kame matar mai suna Aisha Ali da ake zargi da aikata mummunan laifin.

DABO FM ta rawaito rundunar ‘yan sandan jihar Kano tace matar da ake zargi ta tattara nata tayi jihar Jigawa, jihar da take da makotaka tsakaninta da garin na Dambatta.

Sai dai runudunar ta bayyana cewa cikin hadin gwiwar ‘yan sandan dake ran gadi a garin Babura na jihar Jigawa sunyi nasarar kame wannan baiwar Allah a gurin da ta buya.

Mai magana da yawun rundunar, DSP Haruna Abdullahi Kiyawa ne ya bayyana haka a wata takarda mai lamba CZ: 57 00/KS/PRD/VOL.3/72 da ya fitarwa manema labarai a ranar Litinin.

Yace tini dai kwamishinan yan sanda jihar Kano ya bada umarnin dawo da ita zuwa cigibiyar Manyan laifuka domin cigaba da bincike.

Inda ya bada tabbacin tisa keyar Aisha Ali zuwa gaban Kuliya da zarar sun kammala bincike.

Daga karshe dai rundunar tayi kira ga al’ummar Kano da kewaye da su rika gaggauta sanar da ‘yan sanda mafi kusa dasu a duk lokacin da aka aikata wani laifi.

Idan ba’a manta ba dai a ranar 14 ga watan Julin 2019 ne aka samu rahotan wata mata mai suna Aisha Ali wacce ake zargin zubawa mijinta ruwan zafi saboda shirin da yakeyi na karin aure.Karin Labarai

Sabbi daga Blog