Labarai

Yanzu Yanzu: An kwantar da Abba Kyari a wani asibitin jihar Legas

Wani rahoton dake zuwa mana ya tabbatar likitoci sun kwantar da shugaban ma’aikatan Najeriya, Abba Kyari a wani kebebben wuri kan gado domin ya huta bayan samun sa da cutar Covid-19 lokacin da ya shigo Najeriya daga kasar Birtaniya.

Majiyar DABO FM daga bakin iyalan Abba Kyarin su suka bayyana hakan, susun kara da cewa yana warwarewa daga wannan cuta ta Coronavirus, kamar yadda TheCable ta fitar.

“Tin bayan tabbatar da kamuwa da cutar, yayi danyi tari wanda ya tada hankali, da wasu alamu na cutar amma ba ciwon kirji bane, shine dalilin da aka maida shi wajen kulawa ta musamman na wanda suka kamu da cutar dake Ikkon jihar Legas.” Kamar yadda dan uwansa ya bayyana mana.

“Amma har yanzu babu zazzabi mai zafi, ko matsalar yin numfashi da kyar, shine dalilin da ya sa muke ganin yana samun sauki a yanzu haka.”

Karin Labarai

UA-131299779-2