Home LabaraiƊiyar Buhari ta dawo gida bayan kwana 14 a keɓe, bisa zargin tana dauke da cutar Covid-19

Ɗiyar Buhari ta dawo gida bayan kwana 14 a keɓe, bisa zargin tana dauke da cutar Covid-19

by Muhammad Isma’il Makama
0 comments

Yar gidan shugaban kasa, Muhammadu Buhari ta dawo cikin iyalin ta bayan share kwanaki 14 domin zargin tana dauke da cutar Coronavirus bayan dawowar ta daga kasar Birtaniya, wanda likitoci suka tabbatar bata kamu ba.

Rahotan Dabo FM ya bayyana wannan na zuwa ne bayan mai dakin shugaban kasa, Aisha Buhari ta tabbatar a shafinta na Twitter cikin daren jiya Alhamis da mislin karfe 9 na dare.

Diyar huharin dai ta dawo Najeriya ne daga kasar Burtaniya a ranar 19 ga watan Mayu, inda daga nan aka kebe ta bata hadu dai iyali ba har tsahin kwana 14.

Cikin Garin ciki, Aisha Buhari ta bayyana cewa ” Wannan abin farinciki ne tare da godiya ga Mahalicco ta ya tabbatar Diya ta bata kamu da cutar Coronavirus ba, Kuma ina addua Allah ya bawa wanda suka kamu lafiya.”

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00