Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya kara sassauta dokar kulle da karin rana guda.
Rahoton DABO FM ya bayyana hakan ne ta wata sanarwa da mai bawa gwamanan shawara, Abubakar Aminu Ibrahim ya fitar a yammacin Lahadi, wanda yake sanarda gwamnan ya kara ranar Litinin cikin jerin ranakun da za’a dinga bude gari.
Abubakar ya bayyana cewa “Mai Girma Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR ya amince da sassauta ranar Litinin a matsayin ranar fita wanda yanzu ze kasance ranakun Litinin, Laraba, Juma’a, Lahadi sune ranakun fita daga karfe 6 na safe zuwa 6 na yamma.”
Ya kara da cewa “Gwamna yakara kira ga Jama’a musamman yan Kasuwa da sucigaba da bin dokokin da Jamian Lafiya suka bayar na sanya safar fuska da rarrabuwa tsakani.”
Sai dai kuma wannan na zuwa ne bayan jihar ta Kano ta samu masu dauke da cutar Korona fiye da 40, wanda jihar tayi dan kwanaki lambobin masu kamuwa da cutar yayi kasa, zuwa yanzu dai fiye da mutum dubu sun kamu da annobar a Kano.
