Labarai Wasanni

Yanzunnan: Shahararren dan wasan Juventus, Dybala da matarsa sun kamu da cutar Coronavirus

Dan wasan Juventus, Paulo Dybala dan asalin Argentina kuma gogaggen dan wasan da ake ji dashi a duniya ya tabbatar da ya karbi saka makon gwajin da aka yi masa a kan cutar Coronavirus, wanda ya bayyana ya kamu da cutar.

Majiyar Dabo FM ta tabbatar da Rahoton Wanda ya wallafa a shafinsa na Twitter, Dybala yace zuwa yanzu yana cikin koshi lafiya amma yana dauke da cutar COVID-19, inda yace yana godiya da masu masa jaje da cikin wannan mummunan halin daya fada, Wanda ya fitar a ranar Asabar.

Majiyar da ta fito daga kungiyar kwallan kafa ta Juventus ta tabbatar da cewa an keba dan wasan fiya da kwana 10 da suka wuce Duke Yi masa gwaje gwaje, tin a ranar 11 Ga Maris.

Karin Labarai

UA-131299779-2