Labarai

Rahoton Dabo FM na siyar da litar fetir a N143, yasa gidajen mai sun gyara litar su zuwa N125

Bayan wasu rahotannin da suka fita na wasu gidajen saida man fetir a kan sama da naira 143, DABO FM ta ziyarci gidajen man fetir dake jihar Kano domin ganin wace wainar suke toya wa, shin sun bi umarnin Gwamnatin ko kuwa.

Wakilin DABO FM ya ziyarci gidan man Aliko Oil Wanda ke daura da jami’ar Maitama Sule University, inda ya tattauna daya daga ma’aikatan gidan man, Inuwa Yahaya, wanda ya tabbatar mana da cewa su tin ranar da akayi dokar suka rage kudin man su zuwa N125 kamar yadda gwamnati ta bada umarni domin saukakawa talakawa.

Daga nan wakilin mu ya ziyar ci gidan man A.G.Y.L Oil, inda shima ya samu tattaunawa da ma’aikacin gidan man, Muhammad Sani Gwammaja, wanda shima ya tabbatar mana tini suma suka rage kudin man nasu zuwa N125.

Karin Labarai

UA-131299779-2