Labarai

Za’a bawa mutumin da ya bukaci a bashi kasonshi na kasafin kudin Najeriya hakkinshi – Bashir Ahmad

A cikin makon da muke ciki ne dai, faifan bidiyo na wani bawan Allah dan jihar Jigawa ya nemi shugaba Buhari da ya bashi kasonshi na ciki kasafin kudin shekarar 2020.

Inda ya bayyana cewa baya bukatar dukkanin ayyukan da shugaban ya lissafa zai yi a cikin kasafin kudin.

A nashi bangaren, Bashir Ahmad, mataimakin shugaba Buhari a fannin yada labaran kafafen sada zumunta, ya alkauranta biyan wannan bawan Allah kasonshi na kasafin kudin.

DABO FM ta tabbatar da Bashir Ahmad yana cewa; A lissafi na da nayi, idan za’a raba tiriliyan 10 ga ‘yan Najeriya miliyan 200, kowanne zai samu N51,000”

Da yake bayyana a shafinshi na Twitter, Bashir Ahmad, ya alkauranta bawa bawan Allah n nan N50,000.

Sai dai yace zai bashi kudin ne domin samun nutsuwa da kuma kwarin gwiwar cigaba da sana’arshi cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya.

Daga shafin na Twitter, Sani Ahmad Kaitafi da dan uwanshi, sun alkauranta bada tasu gudunmawar ta Naira 45,000.

Tini dai Bashir Ahmad, ya ayyana ya riski wanda zai yi masa iso domin sada Kwamaret da kudaden da suka alkauranta bashi.

UA-131299779-2