0
Ahmad Rufa’i, dan majalissar dokokin jihar Kwara mai wakiltar karamar hukumar Patigi ya rasu da safiyar yau Talata.
Sanarwar ta fito daga kakakin majalissar jihar, Salihu Danladi ta hannun mataimakinshi na fagen yada labarai, Ibrahim Shariff.
Ahmad Rufa’i ya rasu ne bayan fama da yar gajeriyar rashin lafiya wacce tayi ajalinshi a asibitin koyarwa na Jami’ar Ilori.
