Labarai

Zamfara: Bincike ya nuna Abdul’aziz Yari ya bannatar da sama da Naira biliyan 250

Kwamitin karbar mulkin wanda gwamna jihar Zamfara, Bello Matawalle ya kafa a zargi tsohon gwamnan jihar Abdulaziz Yari da bannatar da tsabar kudi na Naira biliyan N251,849,482.50

Shugaban kwamitin tare da tsohon mataimakin gwamnan jihar Ibrahim Wakala ne suka bayyanawa manema labarai a ranar Litinin.

Wakkala yace; ” A kwamiti na wanda muke kokarin binciko abubuwa da wasu hakkoki da tsohuwar gwamntin gwamna Abdula’ziz Yari ta bari a bayanan da kwamitin da Yari ya kafa ya bayar lokacin mika mulki.”

“Mun bankado daga kwamitin da Yari ya kafa cewa akwai Naira biliyan 250 da ba’a fadi me akayi da ita ba.”

“Wannan ya hada wasu kudaden wasu ayyukan da ake gudanarwa guda 462 wanda akeyi akan N151,190,477,572.02 tare kin saka kudi a asusun ”National Housing Fund” da N1,431,645,305.99 na kudaden ma’aikatan da suka ajiye aikinsu da ba’a biya ba

Cikakken rahotan yana shigowa………..

Karin Labarai

Masu Alaka

Abdulaziz Yari ya mikawa Matawalle takardun mulkin jihar Zamfara

Dabo Online

Abdulaziz Yari ‘ya gina rijiyar birtsatsai kan naira miliyan 325’

Dabo Online

EFCC sun kai sumame gidan Abdulaziz Yari na Zamfara

Dabo Online

APC ta shirya korar Abdul’aziz Yari daga jami’iyyar

Dabo Online
UA-131299779-2