Labarai

Bazai yiwuwa ayi zaben da babu kuskure ba – Shugaban INEC

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya INEC, Farfesa Mahmud Yakubu, ya bayyana cewa babu wani tsarin zabe da yake cikakke da babu kuskure a ciki.

SHugaban ya bayanna haka ne a yayin ganawarshi don tattara bayanai akan yadda aka gudanar da zaben 2019 tare da manyan ma’aikata da sukayi aikin zaben guda 380 masu kula da rumfunan zabe a fadin tarayyar NAjeriya.

DABO FM ta tattaro cewa; Farfesa Yakubu yayi kira da ma’aikatan da su bayyana dukkanin wani kalubale da suka gani inda ya bayyana cewa babu wani zabe da yake wanda babu kuskure a ciki.

“Suka da kalubalantar yadda aka gudanar da zabe sai taimakawa kasar nan wajen inganta tsarin zaben. Ina kiranku da ku same sakewa don bawa hukumar INEC shawara.”

“Inda ya kamata a soke mu ko mu soki kanmu. Ina rokon ku da kuyi. Kulli ina fada cewa, abokanka zasu soke ka amma makiya sai dai su kushe ka. Amma sai da suka ake iya samun tafiyar aiki mai kyau.”

“Babu wata tsarin dimokradiya da tsarin zabe da yake babu kuskure. Dukkan wani tsarin aiki tafiya yakeyi. Dan haka ina kiranku da ku bada wani hangenku, shawarwari akan dukkanin hanyoyin gudanar da zabe dama zaben gabaki daya.”

Ku fada kanku tsaye, kuna da kariyar shugaban hukumar zabe, kuma duk abinda kuka fada, baza’a tuhume ku ba.” – Inji Farfesa Yakubu

Ya kara da cewa shirye-shiryen zabubbuka, sufurin ma’aikata, bude rumfunan zabe tare daidata dukkanin rumfunan zabe a ranakun da ake gudanar da zabe ya rataya a wuyan baturen zabe (EOs).

“Duk abinda zamu ji daga bakin wadansa kan yacce a gudanar da zaben Najeriya bai kai kamar yacce zamuji daga wajen wadanda su sukayi ruwa da tsaki har aka gudanar da zabbukan a kowacce rumfar zabe ba.”

Shima a nashi bangaren, Kwamishina kuma shugaban kwamitin tsare-tsare da lura da ayyuka na hukumar, Dr Mustafa Lecky, yace ganawar zata saka su fahimci yacce aka gudanar da zaben 2019 tare da taimakawa wajen yin gyarraki don inganta zaben 2023.

Karin Labarai

Masu Alaka

Yanzu-yanzu: INEC ta soke jam’iyyun siyasa 74

Muhammad Isma’il Makama

Akwai yiwuwar INEC ta soke zaben Zamfara bayan ganawar gaggawa da jami’iyyar APC tayi

Dabo Online

INEC ta kwace takarda shaidar cin zabe daga ‘dan majalissar APC a jihar Ondo

Dabo Online

Kotu ta daure babban jami’in INEC shekaru 6 bisa hannu a cikin karbar cin hancin miliyan 45

Dabo Online

Jerin sunayen jam’iyyu 18 da suka tsallake siradin hukumar INEC

Muhammad Isma’il Makama

Baza’a dena amfani da na’urar Card Reader ba – Hukumar INEC

UA-131299779-2