Ra'ayoyi

Zato Akan Buharin 2015: Nazata Buhari bazaiyi cuta ba, Daga IG Wala

Dan gwagwarmaya kuma dan kasuwa, Ibrahim Garba da aka fi sani da IG Wala yayi rubutu da suke nuna cire tsammaninshi ga mulkin shugaba Muhammadu Buhari.

IG ya kasancewa dan gwagwarmayar tabbatar da cin zaben shugaba Buhari, yana daga cikin ‘yan kungiyar ”Bring Back Our Girls” wadanda sukayi fafutuka wajen ganin an tseratar da ‘yan matan Chibok.

IG Wala yace:

Wallahi Wallahi Wallahi
ZATON DA NAYI AKAN BUHARI!

A 2015, na dauka Baba Buhari zai zo ne ya ja layi tsakanin abinda ya taras da abinda zai yi a gaba:

-Babu cuta ba cutarwa a wajen Kasafin Kudi.- Babu Dan Sandan da zai sake cin hanci ko karban nagoro.
– Babu Mai rike da ofishin Gwamnati da zai saci kudi ta hanyan bada kwangila wa kampanoni a boye ko akawo masa nashi kaso a boye.
– Zai tsara yadda kudaden Sojoji da duk wanda ke fagen yaki ko aiki zai shiga hannun su ba tare da sun koka ba balle kuma ma ace suna kukan an kyale su babu kulawa.
– Zai dauko tsarin gina Makrantu da Ma’aikatu, haka kuma zai iya tafiyar da Gwamnonin Jihohi da su bi irin tsarin da zai sa a kaiga gaci baki daya.
– Tsaro zai samu saboda yanda zai inganta rayuwar jami’an staro da kuma horas da su da kulawa.
– Bangaren Shariya kuwa, za’a zabtare duk wanda yayi kaurin suna wajen lalata tsari da cin hanci da rashawa ba domin yana tare da yan adawa ko gwamnati ba.
– Na dauka zai yi aiki da kwararru ba abokan siyasa da yan’uwa wadanda baza a iya musu magana kan barna ko rashin bin tsarin doka ba.
– Maganan abinda ya shafi rayuwan talaka, kaman su wutan lantarki da man fetur da asibibitoci, na dauka wannan kam tilas ne yayi abinda duniya zata jinjina masa.

SABODA SHI KADAI NE A CIKIN SHUGABANNI DA SUKA SAURA DA RAI MUKE KYAUTATA ZATO A KANSU. AMMA SAI GASHI MUNA KUKA MUNA CEWA “BA ASO HAKA BA”!

IG Wala

Karin Labarai

Masu Alaka

Buhari zai jagoranci bude ayyukan gwamnatin jihar Gombe a yau Litinin

Dabo Online

Gwamnatin Buhari ta samar da ayyukan yi miliyan 12

Dabo Online

Murnar Lashe Zaben Buhari: Matashin daya fara tattaki daga Kebbi zuwa Abuja domin taya Buhari murna

Nan gaba duk dan takarar shugaban kasar da yazo yana muku kuka to kuyi ta kanku -Shehu Sani

Muhammad Isma’il Makama

Dama can nasan Ganduje ne yaci zaben Kano -Buhari

Muhammad Isma’il Makama

‘Yan Najeriya sun yanke hukunci, NNPC ta huta?, Buhari yaci zabe.

Dangalan Muhammad Aliyu
UA-131299779-2