Ra'ayoyi

Zuwa ga Shugaba Buhari: Shekaru 4 Kenan, Chanjin da muke jira yaki zuwa, Daga Nasiru Salisu Zango

Wasika zuwa ga Shugaba Muhammadu Buhari.

Daga Salisu Nasiru Zango.

“Ina fatan Shugaban mu yana cikin koshin lafiya, koda yake wannan a bayyane yake domin yawan tafiye tafiye da Baba ke yi ‘yar manuniya ce dake nuna cewar Baba garau yake. (Allah ya Karo lafiya).

Ya mai girma shugaban kasa, ina so na shiga sahun ‘Yan Nijeriya da suka dade suna maka fatan alheri tun kafin 2003, lokacin da Ka fara shiga faggen Siyasa, a wancan lokaci galiban mun gaji da mulkin malakahu na jamiyyar PDP muna ganin da zarar Kazo shikenan kukan mu ya kare, amma ga alama abin kamar ba haka yake ba, domin yau shekaru 4 kenan chanjin da muke ta jira bai karaso ba, koma Dai yazo amma mutane da yawa basu ga ta sauya zani ba.

Talauci da fatara sun karu, dubban mutane suna kwana cikin su babu abinci, kudin makaranta na gagarar iyaye. Arziki ya koma hannun wasu tsiraru daga su sai ahalinsu.

Ya mai girma shugaban kasa ina rokon ka ka sa ayi maka bincike na gaskiya lan halin talaka ke ciki wallahi wallahi idan mashawartan ka suna gaya maka cewar komai lafiya, to ba gaskiya suke fada maka ba. Domin wallahi abinci ya tasamma gagarar talaka, da yawa mutane sun rasa ayyukan yi, tsananin kullum karuwa yake har ma wasu sun fara tunanin gwamma jiya da yau, ina fatan Baba zai duba domin samun sassauci a next level.

Ya mai girma PMB, abban abin fa da ya karya farin jinin Shugaba Jonathan a idon mutanen Arewa cin Najeriya shine rikicinn boko haram, nasan kowa yasan yadda Zamfara ta kama da wuta wannan zamani.

Ina rokon shugaba Muhd Buhari da ya sake duba halin Kunci da talaka ke ciki domin samar masa da sassauci.

Allah ya taimaki Nigeria ya bamu shugabani da zasu sassauta wa Talaka.

Nagode kwarai Allah ya Karawa shugaban kasa lafiya.”

Karin Labarai

Masu Alaka

Talauci ke haddasa rashin zurfafa karatun Matasa a Yau – Ibrahim Garba Umar

Mu’azu A. Albarkawa

Ba Kwankwaso ne basa so ba, cigaban Talaka ne yake musu ciwo – Dangalan Muhammad Aliyu

Dabo Online

Shawarata ga Shugaba Buhari kan yadda za’a magance tsaron Borno da Zamfara, Daga Datti Assalafiy

Dabo Online

Zuwa ga masu neman a baiwa Mata limancin Sallah da nufin ‘Kare hakkin Mata’ daga Bin Ladan Mailittafi

Dabo Online

Rigar ‘Yanci: Dama nasan za’a rina, tallafin Ganduje wajen ruguza Ilimin ‘yan Sakandire, Daga Nazeef Touranki

Dabo Online

Taskar Matasa: Abbas Nabayi, matashi mai zanen da yafi hoton kyamara

Dangalan Muhammad Aliyu
UA-131299779-2