Anyi baikon Yaro dan shekara 17, da Amaryarshi ‘yar 15 a jihar Sokoto

Hotunan baikon Aliyu, yaro dan shekara 17 tare da amaryarshi Aisha, yar shekara 15 ya ja hankalin mutane musamman matasa.

Labarin ya samo asali a wani shafin sada zumunta na shafin Instagram, Northern Blog, inda matasa ‘yan Arewa suke tattauna batutuwa tare da labaran yau da kullin wanda duk masu bibiyar shafin sukan iya aiko da labari tare da hotuna da bidiyo.

 

Aliyu, 17 da Aisha, 15

Da yake tabbatarwa shafin al’amarin, yayan Aliyu, Muhammad,ya bayyana cewa haka tsarin gidansu yake wajen yin auren wuri.

TALLA

Ya kara da cewa shima an masa aure ne dai dai lokacin da bai wuce shekaru 15-17 ba.

Muhammad a lokacin da yayi nashi auren.

Za dai ayi bikin ne a cikin sati na uku, na watan Afirilun da muke ciki na 2019.

Masu Alaƙa  Zaben Gwamna: Jami'an tsaro sun damke wata mota dankare da kudade a Sokoto

Hotunan Nazbeen Photography

Muhammad Aliyu Dangalan

•Sublime of Fagge's origin. •Apprentice Journalist. •Doctor of Pharmacy student.

%d bloggers like this: