Labarai Siyasa

Zuwan Sanusi Legas: Suna zamansu lafiya, daga saukar sa ya jawo tashin bom – Kwamishinan Ganduje

Kwamishinan ayyuka na jihar Kano, Muaz Magaji ya bayyana komawar Sarki Muhammadu Sanusi II Murabus ce ta kawo tashin bom a jihar Ikko.

Majiyar DABO FM ta bayyana kwamishinan aiyukan na Kano yayi wannan batu ne a fejikan sa na sada zumunta a yammacin Lahadi.

Muazu ya yace “An kaishi Loko sun roki yayi gaban, a Awe suka ce a kaishi ‘further away’ [gaba can], Lagos na zamansu lafiya, daga saukar shi bom ya tashi. Kuma zaku nemi kai dashi ne.”

Sai dai kuma labarin dake ishe mu daga birnin Ikkon ba bom bane ya fashe, silindar gas ce ta fashe tayi kuma sanadiyar mituwar akalla mutum 15.

UA-131299779-2