Labarai

Kwanaki 226 da bacewar Abubakar Idris Dadiyata

Matashi Abubakar Idris Dadiyata ya cika kwanaki 226 tin bayan da wasu da ba’a san ko suwaye ba suka dauke matashin har gida.

Zuwa yanzu, dangin matashin sun kai karar Gwamnatin jihar Kaduna, hukumar DSS reshen jihar Kaduna zuwa gaban kotu domin jin bahasi biyo bayan zarge-zarge da akeyi musu na alhakin daukeshi.

Tin a ranar 1 ga watan Agustar 2019, wasu mutane da ba’a san ko suwaye ba, sukaje har gidan matashi dake jihar Kaduna suka daukeshi, lamarin da yayi sanadiyyar har zuwa yanzu babu labarinshi.

Hukumar DSS da aka zarga tin farkon dauke matashi, ta bayyana cewa bata tsare da matashin, hasalima bata tura jami’anta unguwar su Abu Dadiyata aiki a wannan dare ba.

Dadiyata, malami ne a jami’ar Katsina, ya kasance dan gwagwarmaya da fafutukar ganin gwamnatin APC a Najeriya da jihar Kano su yiwa mutanen da suke jagoranta adalci.

Abubakar Idris, wanda akafi sani da Abu Hanifa Dadiyata, dan Jami’iyyar PDP, mai bin tsari da darikar Kwankwasiyya, tsagin da akeyin ‘Kare-Jini, Biri-Jini’ irin na siyasa tsakaninsu da bangaren gwamnatin jihar Kano na Gandujiyya.

Manyan mutane a Najeriya sunyi Allah-Wadai da kamun matashin, hukumomin kare hakkin dan Adam na duniya sun biye musu sahu wajen kiran wadanda suke tsare da shi su sake shi.

Jagora a jami’iyyar APC, Alhaji Buba Galadima, ya zargi wani gwamnan Arewa wanda bai fadi sunanshi ba a matsayin wanda yake da hannu wajen tsare maatashin.

Masu Alaka

Talauci ke haddasa rashin zurfafa karatun Matasa a Yau – Ibrahim Garba Umar

Mu’azu A. Albarkawa

Tsohon shugaban Majalisar Matasan Nijeriya yayi kira ga Matasa su guji siyasar ‘A mutu ko ayi Rai’

Mu’azu A. Albarkawa

Gidauniyar wasu ‘yan mata a Kano ta kai tallafin kayan abinci da tufafi zuwa gidan marayu da gidan yari

Dabo Online

Ko Sarkin Kano da Ganduje sun shirya ya kamata a kammala bincike – Barr Abba Hikima

Dabo Online

#PrayforDadiyata: Kwanaki 10 da bacewar Abu Hanifa Dadiyata ‘Kwankwasiyya’

Dabo Online

Mulkin APC: Zaben2019 ‘Inconclusive’, Jamb 2019 ‘Inconclusive’, Daga Dangalan Muhammad Aliyu

Dabo Online
UA-131299779-2