/

Buhari ya yi wa Najeriya ƙamshin mutuwa – PDP ta nemi Buhari ya aje aiki

Karatun minti 1
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta nemi shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya sauka daka mukamin shugabancin kasar, inda ta bayyana Najeriya karkashin Buhari kamar majiyyacin dake bukatar injin shakar iska ne domin ya rayu.

Rahoton DABO FM ya bayyana hakan na zuwa ne ta bakin shugaban jam’iyyar na kasa, Uche Secondus cikin wani taron manema labarai da jam’iyyar ke gudanarwa a babban birnin tarayyar Abuja.

Mista Secondus ya kara da cewa “Rashawa ta baibaye hukumomin gwamnati karkashin mulkin Buhari, kamar yadda kowa yasan yanzu akwai badakaloli a hukumomin NDDC, MIC, NEDC, NSITF, EFCC dama wasu da dama.”

Ire-iren wannan badakalolin na kuma fallasa duba da wata sanarwa da majalisar kasa ta fitar na kafa kwamiti da zai bincike hukumar bunkasa bangaren Arewa maso Gabas, majalisar ta zargi hukumar da kashe fiye da miliyan dubu 100 ba bisa ka’ida ba.

 

Karin Labarai

Sabbi daga Blog