/

Yanzu-yanzu: Kotu ta kwace kujerar dan majalisar APC a kano, ta ba wa PDP

Karatun minti 1

Kotu a jihar Kano ta kwace kujerar dan majalisar jiha mai wakiltar karamar hukumar Rogo karkashin jam’iyyar APC, Magaji Dahiru Zarewa.

Rahoton DABO FM ya bayyana cewa nan take kotun ta umarci hukumar zabe ta baiwa wanda yake biye masa a matsyi na biyu, Jibril Ismail Falgore shaidar cin zabe.

Wannan ya biyo bayan karar da dan takarar jam’iyyar PDP ya shigar na cewa sam dan majalisa Zarewa bai cancanci samu nasara ba.

Karar ta bayyana cewa dan majalisar bai aje mukaminsa na shugaban hukumar kula da shigo da magunguna da sauran ababen sha na jihar Kano kwanaki 30 kafin zabe ba, kamar yadda yake a dokar tsayawa takara ta INEC.

Kotun kuma ta umarci magatakardar majalisar jiha ya rantsar da Jibril Falgore nan take ba tare d bata lokaci ba.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog