Gidauniyar Hadeeyatul Khair da wasu mata a jihar Kano suka kafa ta kai tallafin kayan abinci da tufafi zuwa gidan marayu da gidan yari a jihar Kano.
A ranar 7 ga watan Julin 2019 ne dai gidauniyar ta kai ziyararta ta farko zuwa gidan Marayu dake Nassarawa a jihar Kano, inda suka rarraba kayan abinci, kayan sakawa dama daffafen abinci domin ciyar da mazauna gidan.
Kayayyakin sun hadar da Sabulan wanki, Sabulan wanka, Madara, Biskit, Chizi, Lemuka da Gurasa.

Duk dai a ranar 7 ga watan Juli, Gidauniyar Hadeeyatul Khair ta kai ziyarar tallafin zuwa gidan yari dake Goron Dutse ta jihar Kano.

Shugabar hulda da jama’a ta gidauniyar, Pharm Rukayya Kabir Abbas ta bayyanawa DABO FM cewa sun kafa gidauniyar ne domin bada tasu gudunmawar ga tallafawa marasa karfi da niyar rage musu radadin da zafin rayuwa.



