Home Labarai‘Yan sanda ne suka kashe mataimakin kwamishinansu da kansu, suka kashe mana mutum 11 – Shi’a

‘Yan sanda ne suka kashe mataimakin kwamishinansu da kansu, suka kashe mana mutum 11 – Shi’a

by Dabo Online
0 comments

Kungiyar Shi’a ta nesanta kanta daga rahotanni da aka bayyana su a matsayin masu alhaki a kisan mataimakin kwamishinan yan sanda a Abuja.

Shi’a tace, ‘yan sanda da kansu suka kashe jami’in tare da ‘yan Shi’a 11.

A ranar Litinin ne rundunar ‘yan sanda ta bayyana cewa ‘yan kungiyar Shi’a sun harbe DCP Usman Umar a lokacin da suke gudanar da Zanga-zanga a Abuja.

Sai dai mai magana da yawun Shi’, Ibrahim Musa ya nesanta kungiyar da yin amfani da bindigogi.

Yace an farmusu ne a lokacin da suke gudanar da zanga-zangar Lumana.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00