Tue. Nov 19th, 2019

Dabo FM Online

World’s First pure Hausa online Radio

Abba Gida-Gida da PDP sun gabatar da hujjoji 241 na kalubalantar zaben Ganduje

2 min read

Jami’iyyar PDP reshen jihar Kano tare da dan takarar gwamnanta, Abba Kabir Yusuf sun nuna hujjoji 241 da shaidun da yasa suke kalubalantar nasarar Gwamna Ganduje a zaben da aka gudanar watan Maris na 2019.

DABO FM ta rawaito cewa Abba Gida Gida da jami’iyyarshi ta PDP dai suna kalubalantar zaben da gwamnan jihar Kano, Dr Ganduje ya lashe a zaben da aka gudanar a watan Maris 2019.

PDP da Abba suna kalubalantar Ganduje, APC da INEC.

Lauyan masu kara, Mista Adeboyega Owomolo, SAN, ya nuna hujjojin a gaban kotu inda ya kara da cewa a shirye suke da sake kawo kari domin tabbatar da kalubalantar da sukeyi gaskiya ne.

DABO FM ta rawaito cewa lauya Owomolo ya cewa kotu cewa a cikin hujjojin nasu akwai kwafin takardun a akwatinan zabe na EC8As, EC8Bs daga karamar hukumar Albasu, Bebeji, Bichi, Danbatta, Garuj Malam, Gwarzo, Karaye, Kura, Madobi, Nassarawa, Rano, Rogo, Sumaila, Tudun Wada da Warawa da sauran kananan hukumomi.

Lauyoyin wadanda ake kara (APC da Ganduje) Offiong da Ahmad Raji sunki amincewa da hujjojin.

Offiong ya bayyanawa kotu cewa lauyoyin PDP sun shigo da jakunkuna ne kawai ba takardun zabe na gaskiya ba.

“Masu kara basu bamu takardun mu gani ba, sun shigo da jakunkuna ne kawai, ina da damuwa akan abinda yake cikin takardun” – Cewar Lauyan APC, Offiong.

A nata bangaren, mai shari’a Halima Shamaki, shugabar alkalan kotun zaben, tayi watsi da maganar lauyan APC, ta karbi hujjojin da PDP ta gabatar, ta kuma dage cigaba da sauraron karar zuwa 23 ga watan Yulin 2019.

©2019 Dabo FM Online. Sponsored by Dabo Media Group | Newsphere by AF themes.