Home LabaraiKungiyar Izala tayi kiran Sanatoci da kada su tantance Ministocin da suke ‘yan Shi’a

Kungiyar Izala tayi kiran Sanatoci da kada su tantance Ministocin da suke ‘yan Shi’a

by Dabo Online
0 comments

Kungiyar Jama’atul Izalatul Bidi’a wa ikamatussunah tayi kira ga Majalissar Dattijai da kada su tantance ‘yan Shi’ar da sunansu ya fito a jerin sunayen da shugaba Buhari ya aikewa majalissar.

Shugaban gamayyar malaman kungiyar, Sheikh Sani Yahaya Jingir ne ya bayyana haka a wata hirarshi da manema labarai a garin Jos.

Da yake tsokaci akan rikicin dake tsakanin jami’an tsaron da kungiyar Shi’a, Sheikh Jingir yace yakamata kada majalissar ta tantance ‘yan shi’ar dake cikin jerin sunayen.

DABO FM ta rawaito daga Daily Nigerian cewa; Sheikh Jingir bai bayyana sunan kowa ba sai dai yace “Mun gane cewa akwai ‘yan shi’a a cikinsu, muna kira da kada a tantance su.”

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00