Home LabaraiKu bamu Al-Zakzaky zamu kula da lafiyarshi – Iran ta fadawa Najeriya

Ku bamu Al-Zakzaky zamu kula da lafiyarshi – Iran ta fadawa Najeriya

by Dabo Online
0 comments

Babban mai shari’ar gwamnati na kasar Iran, Montazeri, yayi kira da gwamnatin Najeriya da ta basu Zakzaky don kula da lafiyarshi.

Montazeri ya kara kira ga kotu da ta kyale Sheikh Zakzaky ta tafi neman lafiya kamar yacce ya bukata.

DABO FM ta binciko cewa Jaridar AhlulBayt ta kasar Iran ta rawaito cewa; Muhammad Montazeri ya bayyana haka ne wata takarda da ya fitar ranar Asabar.

“A matsayi na, na babban mai shari’a a kasar Iran, ina kira ga bangarorin shari’ari Najeriya da suyi abinda ya kamata wajen zama masu cin gashin kansu domin baiwa dan kasa (Zakzaky) da yake tsare ‘yanci tare da turo mana shi zuwa kasar Iran domin kula da lafiyarshi.

Tin dai a shekarar 2015, shugaban kungiyar ‘yan uwa musulmi ta Najeriya, Sheikh Ibrahim Al Zakzaky yake tsare a hannun hukumomin Najeriya.

Hakan ya san ‘ya yan kungiyar suke ta yin zanga-zanga a garin Abuja domin ganin an sake musu shugaban da suke cewa ana tsare dashi ba bisa ka’i’da ba.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00