Home Labarai‘Dan Najeriya ya kammala karatu da sakamako mafi kyau a Jami’ar kasar Indiya

‘Dan Najeriya ya kammala karatu da sakamako mafi kyau a Jami’ar kasar Indiya

by Dabo Online
0 comments

Dan Najeriya ya fita da sakamakon mafi kyawu a wata Jami’a dake kasar Indiya.

Dalibin mai suna Ibrahim Sa’id Naboi, dan asalin jihar Adamawa ya samu lambar yabo tare da girmamawa bisa fita da sakamakon Digiri mai lamba ta daya.

Ibrahim, wanda ya kammala karatun nashi a Jami’ar NIMS dake jihar Rajasthan ta kasar Indiya, ya bayyanawa DABO FM irin farincikin da ya samu kanshi a ciki bisa nasarar da ya samu.

Ya kuma yi kira da sauran dalibai musamman wadanda suke karatu a kasar waje da su cigaba da dagewa wajen yin kokari a wajen karatunsu domin daga darajar Najeriya a idanun duniya.

Ibrahim dai ya kammala karatun “International Relation” a shekarar 2019 tin bayan farawarshi a shekarar 2016.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00