A cigaba da shirin DABO FM na binciko hazikan matasan Arewa wadanda suke da baiwa a fannoni daban daban, yau mun zakulo wani matashi da yake zane-zane.
Abbas Haruna Nabayi, wani matashi ne mai shekaru 21 dan asalin jihar Kano, wanda yake da baiwar zane-zane da Fenciri.
Abbas Nabayi ya kwarance wajen yin zanen baki da fari wanda har ya kai ga yin zanen da yake siyarwa.
Zuwa yanzu matashin ya zana wasu daga cikin manyan mutanen arewa hadi da sanannu ‘yan wasan kwallon kafa dana kwaikwaiyo, wadanda suka hada da Alhaji Aliko Dangote, Haj Aisha Buhari, Ahmad Musa da Aishatul Humaira.
Ga wasu daga cikin hotunan zanen Abbas Nabayi.

