Home LabaraiZamu tabbata fitar da ‘Yan Najeriya miliyan 50 daga kunchin Talauci – Dr Pantami

Zamu tabbata fitar da ‘Yan Najeriya miliyan 50 daga kunchin Talauci – Dr Pantami

by Dabo Online
0 comments

Ministan Sadarwar Najeriya, Dakta Isa Ali Pantami, ya bayyana cewa zasu yi aiki tukuru wajen cika burin shugaban Najeriya, Muhhammadu Buhari domin ccire yan Najeriya miliyan 50 daga kangin Talaucin da yayi musu katutu.

Ministan ya bayyana haka a ranar da ya fara ziyarar aiki zuwa ma’aikatar Sadarwar, awanni kada bayan rantsar da shi a matsayin sabon Jami’in da zai shugabanci ma’aikatar.

A lokacin ziyarar, Dakta Pantami yayi kira ga ma’aikatan ma’aaikatar da suyi aiki tukuru su kuma daga wajen cika umarnin shugaban kasa wajen cire al’ummar Najeriya a kalla miliyan 50 daga talauci.

“ Matsalolin da Najeriya ke fama dasu ba a boye suke ba. Babu bukatar sai na lissafa su a nan. Haka zalika mun san irin muhimmiyar rawar da hanyar sadarwa ta ICT za ta iya takawa wurin magance matsalolin.”

“ A don haka ina rokon ko wannenku da yayi shirin aiki sosai da sosai. Ko shakka babu na aminta da abinda sakatare na ya fadi game da umarnin Shugaban kasa cewa mu tabbata mu cire mutum miliyan 50 daga talauci nan da ‘yan shekaru kadan masu zuwa.

“ Wannan abu ne wanda zamu iya yi, kuma ina da yakinin cewa hakarmu za ta cinma ruwa dangane da wannan magana. Akwai kalubale mai tarin yawa dangane da ICT haka kuma akwai hanyoyi na fitar da sabbin ababe. Don haka zamu yi iya bakin kokarinmu mu ga cewa mun cikawa Shugaban kasa bukatarsa.” – Dakta Pantami. –Fassara Sashin Hausa na Legit.ng.

Sai dai a shafin Twitter na Ministan, ya bayyana cewa an sabawa ma’anar maganar tashi tare da cewa “Shawara ce ya bayar” ba aikin tabbaci ba.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00