Ra'ayoyi

Zuwa ga masu neman a baiwa Mata limancin Sallah da nufin ‘Kare hakkin Mata’ daga Bin Ladan Mailittafi

Daƙuwata Ga ‘Yan Feminizim!
.
Ina tsaka da sallah, shaiɗan ya hanani sukuni, ban samu ‘nutsuwa’ ba sai da na kyalla ido, na ɗan kai dubana gareta. Masu rájin ƙwato wa mata ‘dannannen haƙƙinsu’ (Feminists) su suka faɗo mun a rai, daga baya, sai na afka kogin tunani, da an daka ta tasu, to da ita ce limamiyar, ya kenan? An ya sallar masallaci mai raunin imani irina a bayan imamiya za ta iya sallatuwa a mamunce kuwa?
.
A shekarar 2005, farfesa Amina Wadud, malamar ‘Islama’, ta limanci maza da mata sallar Juma’a, a ƙasar Amuruka, a birnin Niwyok. A 2008, Osfod sun gayyace ta, ta je har Buritaniya, nan ma ta ja maza da mata limancin sallar Juma’a, a garin Osfod. Da haka- da haka, iskancin Feminizimcinsu a Musulunci, ya cigaba da gudana…
.
Addínu Annasíhah – Musulunci Masalaha Ne:
Limami Rátibi ake da buƙata. Mace ba za ta taɓa zama Rátiba ba (kullum ta limanci Kamsus-Salawati) Ita fa, ba kullu-yaumin take sallar ba. Hana mata limanci, ba zai taɓa zama tauye haƙƙinsu ba a Addinince, a al’adance, haka kuma a matance (ai a zatiyance) uzuransu ba za su lissafu ba, masalahar kansu Maƙaginsu ya duba cikin hikima, domin Shi ba Ya kallafa wa halittarSa wani abu, face Ya san za ta iya yi.


.
…. Mace limamiya sai a sanya ma ta na’iba Kenan? Yau tana masallaci tana limanci, gobe ko jibi, tana gida tana: al’ada, ko jego, ko raino, ko jiyar mara lafiya, ko laulayin ciki, ko jinin biƙi, ko aikace-aikacen gida, ko ta makara, ko ta tafi unguwa, Ita ma na’ibar tata ba za ta taɓa kaɗaituwa daga ɗaya daga cikin waɗannan uzuran ba, sai Musulunci ya yi mata gata, Allah bai ɗora mata ba, don Ya san ba za ta iya ba. A’a bari ma dai sauƙaƙa mata Ya yi, sallarta a gida, ta fi sallarta a masallaci ladaddaki, ayar ku yi zamanku a gidajenku, ba a shafe ta ba. Mace ba za ta taɓa iya fitowa daga gida sau biyar a rana zuwa masallaci, ba tare da mushaƙƙa ba.
.
Lokacin sallah ya yi, mámú suna jiran fitowar limamiyarsu, shiru-shiru:
.
Ashe ta wayi gari da janaba;
Ashe jinin Haila ya zo mata;
Ashe laulayi take yi;
Ashe naƙuda take yi;
Ashe jego take yi;
Ashe jinin Biƙi take yi;
Ashe jinin cuta take yi;
Ashe yaro take ta rarrashi;
Ashe yara take shiryawa;
Ashe girki take yi;
Ashe kwalliya take yi;
Ashe ta tafi unguwa;
Ashe ta yi baƙi;
Ashe ta tafi gida/asibiti jíyá;
Ashe ta tafi gidan biki,
Ashe ta tafi gidan suna,
Ashe ta tafi gidan mutuwa;
Ashe! Ashe!! Ashe…!!!
To a gabatar da na’ibarta ta limanci sallar, ashe, ashe, ashe ita ma hakan take! 
Ashe Musulunci gata ya yi mata?
Ashe masalaharta ce?
Ashe hanin tausayawa ne gareta?


.
Ni dai har na girma, ban san mata suna shan azumi ba, ban san akwai wasu kwanuka da ba sa sallolin Farilla ba, an dai karantar da ni wancananka ne a littafi, amma a aikace ban taɓa ganewa ba, har na bar gida (na yi aure) Kai matarka ma, ina mai tabbatar maka ba za ka san Hailarta ta zo ba, sai tá kámá (ai sai da ƙwaƙƙwaran dalili) Idan haka ɗabi’ar mata take ga Muharramansu, ya kake zaton ninkuwar halin ƙuncin da za su shiga a ruhince, a zahirance, idan bare ya zama masanin kwanukan al’adarsu?
.
Mámú (1) Ya ce: Lafiya kwana biyu limamiya ba ta fitowa sallah?
Mámú (2) Ya ce: Ai ka san a farkon wata take al’adarta.
Mámú (1) Ya ce: Hailar kwana nawa take yi?
Mámú (2) Ya ce: Ba ta wuce kwana biyar, ka zuba ido, gata za ka gan ta a masallaci. 
.
Surar halittar namiji ta sha bamban da ta mace, a yayin da sha’awar namiji take motsowa nan take cikin sakunkuna, da zarar ya ga zatin mace, ita kuma a gunta abin ba haka yake ba. Wannan kaɗai ba zai zama masalahar maza ba? Don guje wa hakan, Shari’a ta hana miji da mata su haɗa sahu. Hikimar hakan ta sanya, mafi sharrin sahun mata; sahunsu na farko, saboda kusancinsa da sahun maza na ƙarshe, sahunsu na ƙarshe ne mafi alherin sahu, saboda nisancinsa da sahun maza, jirkita wancananka, zai ba ka hukuncin sahu-sahu na maza. Akwai matsala babba, kusantuwar namiji da mace.
.
Me kake zato ga ƙaton jarababben gardin da ya tsaya a bayan limamiya; macen ma irin lafiyayyiyar ni’imtacciyar ‘yar Boko-Aƙidar nan, benu ba kya tsufa, ko matashiyar da take kan ganiyarta, ( Idan kun manta, mu ba mu manta yadda kuke ƙyasa malamanku na Boko mata ba) Me zai hana shaiɗan halarto masa da ya riƙa suranta wa kansa ruku’unta da sujjadarta a goho? Ya hau yin zinar ido, da ta tinani da ita, kafin a idar da sallar tini maziyyi ya gama jiƙa gaban wandon almuri. Kai ɗan Feminizim! Hana mace limanci, tsiran Musuluncinka ne. “Lá saláta liman lá wudhú’a lahu.” Kuma “Wa man sallá bigairi wudhú’in, ámidan, fahuwa káfirun. Wal iyázu billáhi”! Ba a san maja-baƙi da fassara ba… Sí-Yú-Létá!
.
#A_Dr_Without_PhD_Bin_Danladi_Mailittafi
20/08/2019

Karin Labarai

Masu Alaka

Rigar ‘Yanci: Dama nasan za’a rina, tallafin Ganduje wajen ruguza Ilimin ‘yan Sakandire, Daga Nazeef Touranki

Dabo Online

Ko Sarkin Kano da Ganduje sun shirya ya kamata a kammala bincike – Barr Abba Hikima

Dabo Online

Kwanaki 217 da bacewar Abubakar Idris Dadiyata

Dabo Online

Kwanaki 257 da bacewar Abubakar Idris Dadiyata

Dabo Online

Daliban Kano sun lashe gasar Kwalliyar Gargajiya ta Jami’ar ABU bayan sunyi ado da Jajayen Huluna

Dabo Online

Kwanaki 226 da bacewar Abubakar Idris Dadiyata

Dabo Online
UA-131299779-2