Home LabaraiMun gaji da gafara Sa bamu ga Kawo ba akan karin Albashin N30,000 – Kungiyar Kwadago

Mun gaji da gafara Sa bamu ga Kawo ba akan karin Albashin N30,000 – Kungiyar Kwadago

by Dabo Online
0 comments

Kungiyar kwadago ta Najeriya tayi watsi da yin Allah wadai da tsaikon fara biyan ma’aikata sabon Albashi na N30,000 da gwamnatin tarayyar Najeriya take yi.

Shugaban kungiyar, Dakta Ayuba Wabba, tare da tsohon Sakataren kungiyar, Dakta Peter Eson, suka sanya hannu a takardar koken tare da yin kira da a gaggauta biyan sabon Albashin.

Daily Nigerian ta rawaito cewa kungiyar tayi zaman yanke wannan hukunci ne a jihar Kano bayan wata ganawa da shugabannin kungiyar sukayi a jihar.

Tin dai watan Afirilun 2019, shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannun aminta da karin albashi daga N18,000 zuwa N30,000 a matsayin mafi karancin Albashi a Najeriya.

“Kwamitin Zartarwar na kungiyar Kwadago tayi Allah wadai da jinkirin biyan sabon Albashin N30,000 da gwamnatin tarayya take yi dama sauran matakan gwamnati.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00