0
Daga cikin mataimaka shuugaba Buhari akan harkokin kafofin sadarwa, Lauretta Onochie, ta bayyana jin dadinta bisa maka gwamnatin jihar Legas da akayi a kotu.
Hakan na zuwa ne bayan da wasu lauyoyi, ciki harda matashin nan Abba Hikima, suka jagoranci shigar da gwamnatin Legas kara bisa tsare yan Arewa 123 a lokacin da suke shiga jihar Legas a makon da ya gabata.
Lauretta Onochie ta bayyana jin dadinta ne a wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter ranar Talatar 3 ga watan Satumbar 2019.
“Matakin da suka dauka na zuwa kotu yayi min dai dai, kuma shine abinda ya dace.”
Hakan zai kawo karshen cin zarafi da ake yiwa wasu yan Najeriya a doran kasar.”
