//
Thursday, April 2

Borno ta doke Kano a zabe na 2 a gasar Kwalliyar Al’adu bayan ayyana zaben farko ‘Inconclusive’

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Rahotanni masu cin karo da juna.

Daliban jihar Borno ne suka lashe zaben gasar kwalliyar gargajiyar al’adun Najeriya da aka gudanar a Jami’ar ABU Zaria.

Rahotan da yaci karo da wanda DABO FM ta wallafa a farko wanda ta bayyana daliban Kano a matsayin wadanda suka lashe zaben na shekarar 2019.

Abinda ya faru!

Ranar 31 ga watan Agusta, 2019, shafin dake shirin gasar al’adu ta jami’ar ABU Zaria ‘ABU Grand Cultural Carnival’ ta wallafa gasar fitar da jihohin da kwalliyarsu tayi fice a jerin kwalliyar dukkanin al’adun da suka taka rawa.

Bayan dogo zabe da fafatawa, jihohin Borno da Kano suk kasance wadanda suka kai ga zagayen karshe na zabe.

Shafin ya sanya zaben a ranar 31, inda kowacce jiha tsakanin Borno da Kano ta samu kashi 50 na kuri’u 7,131 da aka kada a gasar.

Masu Alaƙa  Kwana 161 da daukewar tauye hakki da akayi wa matashi Abubakar Idris ‘Dadiyata’

Anan ne DABO FM, muka fitar da rahoto tare da ayyana jihar Kano a matsayin jihar da ta lashe gasar.

Bayan fitar da rahoton ne cibiyar dake shirya gasar ta sake saka gasar mai tsawon awanni 3 domin sake barje gumi.

A nan ne bayan kada kuri’u 4,473, jihar Borno ta doke jihar Kano da kaso 53 a cikin 100.

DABO FM, Muna so muyi amfani da wannan dama wajen bada hakuri akan labarin da muka wallafa a farko tare da bada tabbacin kaucewa sake faruwar hakan a nan gaba.

Karin Labarai

Share.

About Author

•Sublime of Fagge's origin. •PR Specialist •PharmD candidate

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020