1
‘Yan ta’addan kungiyar Boko Haram sun can suna kone gidajen al’umma a kauyen Mifa da ke karamar hukumar Chibok na jihar Borno.
Wani mazaunin kauyen ya shaidawa The Cable cewa ‘yan ta’addan sun shigo kauyen misalin karfe 8 na dare kuma nan take suka fara bankawa gidajen al’umma wuta.
“Suna kone gidaje a halin yanzu da muke magana da kai, sun zo da yawa a kan babura sun fara kone-kone,” a rahoton TheCable.
“Sun kone gidaje da yawa.”
